About Us   |   Contact Us   |  
Submission  

Fina-Finan Hausa a Mahangar Al’umma: Gyara ko Ɓarna?

DOI : https://doi.org/10.36349/EASJEHL.2020.v03i03.002
PDF
HTML
XML

Wannan takarda mai suna “Fina-Finan Hausa A Mahangar Al’umma: Gyara Ko Ɓarna?” ta yi nazarin wasu fina-finan Hausa tare da bayyana yadda al’umma ke kallon su ta ɓangaren gyara da kuma ɓarnar da suka kawo a cikin al’umma. An rubuta takardar domin faɗakar da al’umma dangane da irin alfanun da fina-finan suka kawo da kuma ayubban da suka haddasa a cikin al’umma baki ɗaya. An yi haka ta hanyar aron bakin al’umma aka ci musu albasa, duk da yake an yi hira da mutane masu yawa a kan irin gyaran da suke ganin fina-finan Hausa suka kawo da kuma matsalolin da suka haddasa. An gano akwai ɗan amfani da ba a rasa ba sai dai illoli sun fi a ƙirga. Abin da ya nuna haka shi ne, duk abin da ya zo ya raba al’umma da halinta na kirki da aka san ta da shi (tarbiyyarta) da kuma sanya ta cikin halin da ba a san ta da shi ba illa ne. Ba wannan kaɗai ba, fina-finan har faɗa suke yi da addinin Bahaushe. Wasu mutane ma ganin suke yi fim bai tsinana wa al’ummar Hausawa komai ba face ci baya. Takardar ta kawo wuraren da aka samu gyara da kuma ɓarnar da fina-finan suka tafka a al’ummar Hausawa tare da misalan da ke tabbatar da hakan. An yi haka domin iyaye su farka daga barcin da suke yi da nuna kula da ‘ya’yansu da na al’umma baki ɗaya domin ɗan Bahaushe na kowa ne a al’adance idan aka yi zancen tarbiyya.

TOP EDITORS

OPEN ACCESS JOURNALS

Dr. Afroza Begum

Lecturer, Dept. of Pharmacology and Therapeutics, Shaheed Monsur Ali Medical College & Hospital, Uttara, Dhaka-1230, Bangladesh

BEST AUTHOR

Of The Month

TRACK YOUR ARTICLE

Enter the Manuscript Reference Number (MRN)
Get Details

Contact us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher)
Nairobi, Kenya


Phone : +91-9365665504
Whatsapp : +91-8724002629
Email : easpublisher@gmail.com

About Us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher) is an international scholar’s publisher for open access scientific journals in both print and online publishing from Kenya. Its aim is to provide scholars ... Read More Here

*This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.

© 2020, All Rights Reserved | SASPR Edu International Pvt. Ltd.

Developed by JM