About Us   |   Contact Us   |  
Submission  

Gani Ga Wane...: Kasuwancin Damfara a Kan Intanet

DOI : https://doi.org/10.36349/easjehl.2024.v07i12.001
PDF
HTML
XML

Samuwar intanet da bunƙasar kasuwancin duniyar intanet sun buɗe wani sabon babin damfara da sunan kasuwanci. An yaudari mutane masu yawa, cikinsu har da Hausawa, kuma ana kan yaudarar wasu. Manufar wannan bincike ita ce bitar wasu daga cikin kasuwancin kan intanet na yaudara da suka ritsa da Hausawa domin kwatanta su da wasu kasuwancin kan intanet da suke da alamar tambaya a kansu a yau. An yi amfani da bitar ƙunshiyar kafafen intanet da shafuka da zaurukan sada zumunta na kasuwancin a matsayin dabarar tattara bayanai. An tantance bayanan tare da samun ƙarin bayani ta hanyar tattaunawa da Hausawan da suke ganau. Falsafar Hausawa ta ‘gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah’ ta yi wa binciken jagoranci. Sakamakon binciken ya nuna cewa, kasuwancin kan intanet na 52u da Anchor waɗanda Hausawa masu yawa suke ciki a yau suna da zubi da tsari iri ɗaya da wasu kasuwancin damfara da suka taɓa rufewa da kuɗaɗen mutane a wajajen 2020 zuwa 2021. Bugu da ƙari, binciken ya fahimci cewa, kwaɗayi yana rufe wa mutane ido yadda suke yaudaruwa da tarkon ‘yan damfara. Daga ƙarshe, binciken ya ba da shawarwarin da suka haɗa da faɗakar da Hausawan da suke hulɗoɗin kasuwancin kan intanet da su mayar da hankali wajen samun cikakken ilimin harƙalla kafin shiga cikinta.

TOP EDITORS

OPEN ACCESS JOURNALS

Dr. Afroza Begum

Lecturer, Dept. of Pharmacology and Therapeutics, Shaheed Monsur Ali Medical College & Hospital, Uttara, Dhaka-1230, Bangladesh

BEST AUTHOR

Of The Month

TRACK YOUR ARTICLE

Enter the Manuscript Reference Number (MRN)
Get Details

Contact us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher)
Nairobi, Kenya


Phone : +91-9365665504
Whatsapp : +91-8724002629
Email : easpublisher@gmail.com

About Us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher) is an international scholar’s publisher for open access scientific journals in both print and online publishing from Kenya. Its aim is to provide scholars ... Read More Here

*This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.

© 2020, All Rights Reserved | SASPR Edu International Pvt. Ltd.

Developed by JM