About Us   |   Contact Us   |  
Submission  

Bori Da Girka A Bahaushen Tunani: Duba Cikin Waƙar Bahaushen Girka Ta Sulaiman A. Tijjani

DOI : https://doi.org/10.36349/easjehl.2021.v04i01.005
PDF
HTML
XML

Tsakure: Sau da dama akan samu dangantaka tsakanin al’ada da adabin Bahaushe. Irin wannan dangantaka ce za a tarar yayin da aka nazarci waƙar Bahaushen Girka ta Sulaiman A. Tijjani. Dalili kuwa shi ne, a cikin waƙar ya zayyano al’amuran da suka shafi al’adar girka daki-daki. Wannan takardar ta mayar da hankali wajen nazarin waƙar domin fito da muhimman kalmomi da Sulaiman Tijjani ya yi amfani da su da ke da alaƙa da al’adar bori da girka. An bi manyan hanyoyi guda biyu domin gudanar da wannan bincike. Hanya ta farko ta shafi nazarce-nazarcen ayyukan da suka gabata masu dangantaka da binciken. Bayan haka kuma, an yi ziyarar gani-da-ido zuwa wuraren da ake gudanar da bori domin samun ingantattun bayanai daga tushe. Sakamakon binciken na nuna cewa, mawaƙin ya yi ƙoƙari wajen samar da bayanai masu inganci game da al’adar girka. Dangane da hakan ne takardar ke ba da shawarar cewa, a ba da ƙaimi wajen nazartar ire-iren waɗannan waƙoƙi da ke ƙunshe da al’adun Hausawa.

TOP EDITORS

OPEN ACCESS JOURNALS

Dr. Afroza Begum

Lecturer, Dept. of Pharmacology and Therapeutics, Shaheed Monsur Ali Medical College & Hospital, Uttara, Dhaka-1230, Bangladesh

BEST AUTHOR

Of The Month

TRACK YOUR ARTICLE

Enter the Manuscript Reference Number (MRN)
Get Details

Contact us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher)
Nairobi, Kenya


Phone : +91-9365665504
Whatsapp : +91-8724002629
Email : easpublisher@gmail.com

About Us


EAS Publisher (East African Scholars Publisher) is an international scholar’s publisher for open access scientific journals in both print and online publishing from Kenya. Its aim is to provide scholars ... Read More Here

*This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial 4.0 International License.

© 2020, All Rights Reserved | SASPR Edu International Pvt. Ltd.

Developed by JM